Darus-sahaba
1jojlxKOMkX9WyteRe4hGfd...5Tlzwos6Wa8pU99NjJEjmoO7lE72qs...P8zLBUI5VEdw01bf9Bj3WN2UJZQ0kMkumqAOI9CU319yy4DVw
Maraba Da Zuwa Wannan
Shafi Mai Al-barka

wanna shafi yana zuwa muku kai tsaye daga masallacin jumu'a
Jami'u Abu hurairah
Dake kurna y'an kifi titin y'an smogal a karamar hukumar dala dake kano Nigeria
kar kashin jagorancin
Sheik Muhammad Sani Uthman Kurna

Home
Karatut-tukan Sheik Muhammad Thani Uthman Kurna
Mata A Musulunci
Bayanin Zakka
Bayanin Azumi
Bayanin Hajji da Umara
Kasuwanci mai ribar gaske
Muhimmin Sako Zuwa ga Ma'aurata
Tsarin Mu'amala A cikin Musulunci
Hakkokin Manzon Allah s a w Akan Alumarsa
Shin hadin kai zai yiwu tsakanin Ahalussunnah da shi a
Wadanna mata aka Haram tawa musulmi da kuma wanda aka Halarta
Hukunce - Hukunce da suka shafi mata
Jinin Al ada ga mata
Jagoran mai wa azi
Adduo in manzon Allah s a w
Falalar Karatun Al-kur'ani
Falalar Sahabbai {R.A}
Falalar Sahabbai {R.A} Daga bakin Imamai
Tarihi
Falalar Ahlulbait daga bakin Ahlussunnah
Tambayoyi masu muhimmanci A cikin Addinin Musulunci
Ayyukan Zuci
Tattaunawa Ta Nitsuwa
Addinin Shi'a
Hukunce-Hukuncen Da Suka Shafi Mata
Karatut-tukan Malamai da Lakcocin su



2014-12-13

-----------------------------------
MUTANEN KUFA
Birnin Kufa shi ne cibiyar Iraqi. Sahabin Annabi (S.A.W) Sa’ad bin Abi Waqqas (R.A), wanda shi ne Kwamandan da ya ci qasashen Iraqi da Farisa da yaqi, shi ya kafa garin da umarnin Sarkin Musulmi Umar bin Khaxxab (R.A) a shekara ta 638 miladiyya. Garin yana kan gavar yamma ta kogin Furat kuma ya zama sansanin soji, kuma cibiyar mulkin Iraqi a zamanin mulkin Halifofi Umar da Usman, Allah ya yarda da su. A lokacin da aka yi wa Ali bin Abi Xalib (R.A) mubaya’a ya zama Halifa, ya xauko fadar mulkinsa daga Madina zuwa Kufa inda ya zauna ya yi mulki har rasuwarsa. Saboda haka a Kufa ne a wancan zamani aka fi samun mabiyan Ali da magoya bayansa na gaskiya da na qarya, wato Musulmi na gari da kuma Rafilawa munafukai. Wannan ya sa a tarihance idan aka ce mutanen Kufa, ko ’yan Kufa, to yawanci Rafilawa ake nufi kai tsaye. Domin tabbatar da wannan, bari ka ji abin da wani mashahurin malamin Shi’a mai suna Baqir Sharif Alqurashi yake faxi: “Lallai Kufa ta kasance mahaifar Shi’a ce, kuma gidan Alawiyyawa (Zuriyar Ali), kuma wannan birni ya nuna qaunarsa ga Ahalul Baiti a tsawon zamani.” – (Duba hayatul Iman Hussain na Baqir Alqurashi, bugu na huxu, mujalladi na 3 shafi na 12).

Halayen Mutanen Kufa:
To bayan mai karatu ya ji daga bakin malaman Shi’a cewa Kufa ita ce tushen Shi’a, kuma gidan masu goyon bayan zuriyar Ali (R.A), bari mu saurari shaidar malaman Rafilawa kuma dangane da halaye da Jawad Muhaddisi, wani qasaitaccen malamin Shi’a na wannan zamani kuma mai yawan rubuce-rubuce, yana faxi dagane da mutanen Kufa: “Daga cikin xabi’un mutanen Kufa da halayensu muna iya yin nuni zuwa abubuwan da ke tafe: Tufka da warwara a alaqa; yawan hilace-hilace; rashin tabbas; tawaye ga masu mulki; rowa da tsananin kwaxayi; gaskata jita-jita da qabilanci…”. Waxannan halaye nasu suka sa Ali (A.S) ya xanxani tasku daga wajensu. Xansa ma Imam Hassan, ya fuskanci yaudara daga wurinsu, kuma a tsakaninsu ne aka kashe Muslim bin Aqil (xan aiken Hussaini) bisa zalunci. Haka nan Hussaini ma an kashe shi a Karbala kusa da Kufa, kuma a hannun rundunar Kufa.” – (Duba Mausu’atu Ashura na Jawa Muhaddisi, bugun Darur Rasulil Akram, Beirut, 1418BH, shafi na 59.

Har ila yau, wani shaihin Rafilawa mai suna Hussaini Kurani yana cewa dangane da ban gaskiyar mutanen Kufa: “Tana yiwuwa a taqaice siffofin imanin mutanen Kufa kamar haka: Zama ga barin taimakon Musulunci, son abin duniya da halin hawainiya a wajen xaukar matakai (wato yawan canja sheqa irin na ’yan siyasar Nijeriya a yau).” – (Duba fi Rihabi Karbala na Husaini Kurani, bugun Darut Ta’aruf, Beirut, 1413BH shafi na 53).

Wannan ita ce shaidar Malaman Rafilawa dangane da irin halayen mutanen Kufa waxanda suke da’awar su mabiyan Ali (R.A) ne masu qaunar sa kuma suna zaune tare da shi a garin da ya zava don ya zama fadarsa. Kuma sirrin kasancewar waxannan mutane haka shi ne cewa ita Shi’a da ma an kafa ta ne musamman don yaqar Musulunci da rusa addini daga ciki, kuma farkon waxanda suka rungumi qungiyar su ne Majusawa da Yahudawa da kuma ’yan tawaye Khawarijawa waxanda suka yi wa Sarkin Musulmi Usman bin Affan tawaye suka kashe shi. Wannan ya sa a ko da yaushe waxannan mutane suke neman kafar tayar da fitina. Kuma wannan ya sa ko da yaushe suna da’awar su masu qaunar Ahalul Baiti ne, amma shugabannin Ahlul Baiti, Ali da zuriyarsa, su suka fi kowa cutuwa da su.

DANGANTAKAR MUTANEN KUFA DA AHALUL BAITI
Dangantakar shugabannin Ahlul Baiti da mutanen Kufa ’yan Shi’a masu cewa su mabiyansu ne, masu qaunar su, ta kasance dangantaka da aka gina a kan yaudara da basarwa da zagon qasa da qafar ungulu ga duk wani qoqari na Ali bin Abi Xalib (R.A) da ’ya’yansa. Kuma bayanin wannan dangantaka filla-filla yana rubuce a cikin littattafan malaman Shi’a, amma mabiyansu ba sa gani, kamar yadda ake cewa a karin magana: “Ga wani abu a kan matar sarki da da ido da ta gani”. Ga alama mabiya tafarkin Shi’a sun rasa ido, don haka suke xora laifin kisan Hussaini a kan Ahalus Sunna, domin da suna da ido da sun ga cewa ba wani ne ya kashe Hussaini ba sai ’yan Shi’a su da kansu. To amma ina ake zancen ido a wajen jahili wanda ba ya iya karanta littafin Larabci saiidan yana da wasali. – (Mai karatu ya nemi kaset mai taken: Tatsuniyar Gadir Khum don ya ji da kunnensa inda madugun Rafilawan Nijeriya, Yakubu Alzakzaki, ya kasa karanta littafi saboda ba shi da wasali). Idan kuwa ba haka ba, to sai dai ya koma ga translation da transliteration.

A nan qasa za mu yi bayanin alaqar ’yan Shi’a da shugabannin Ahalul Baiti xaya da xaya kamar yadda ta zo a littattafan malaman Rafilawa su da kansu.

Dangantakarsu da Ali bin Abi Xalib (R.A):
Mashahurin malamin Shi’an nan wanda ya tattara maganganun Ali bin Abi Xalib da huxubobinsa a cikin littafin Nahajul Balaga, Sharif Alradi, ya rawaito Sarkin Musulmi Ali (R.A) yana kokawa dangane da halayyar mabiyansa mutanen Kufa da mu’amalarsu gare shi. Ya ce: “Ya mazare masu kamar maza, ya masu hankulan jarirai da qwaqwalen ma’abota mundaye. Na so a ce ina ma ban tava ganin ku ba; ban san ku ba. Saninku wallahi ya jawo nadama, ya haifar da fargaba. Allah wadaranku! Kun cika zuciyata da baqin ciki, kun loda qirjina da fushi kuma kun shayar da ni maxin takaici. Kun vata min tsari ta hanyar savawa da basarwa har Quraishawa suna cewa: “Xan Abi Xalib namiji ne gwarzo, amma bai da dabarar yaqi. To ina dabara ga wanda ba a yi wa biyayya?!” – (Duba Nahajul Balaga na Sharif Alradi, bugun Darul Ma’arifa, Beirut, ba tarihi, mujalladi na 1, shafi na 70 – 71).

A wani wurin kuma, ya rawito shi yana cewa: “Al’ummai suna tsoron zaluncin masu mulkinsu, ni kuwa ina tsoron zaluncin mabiyana. Na kira ku zuwa jihadi ba ku fito ba; na umarce ku ba ku bi ba; na kira ku a voye da sarari ba ku amsa ba; na yi muku nashia ba ku karva ba. Haba jama’a! kuna nan kamar ba ku nan? Kuna bayi amma da halin iyayen giji? Ya waxanda jikkunansu suke nan, amma hankulansu sun faku! Ya masu savanin soye-soyen zukata! Ya waxanda aka jarrabi sarakunansu da su! Ni ina bin Allah kuma ku kuna sava masa! Na yi burin wallahi ina ma Mu’awiyya zai yi min musanyen ku irin musanyen dinari da dirhami; sai ya karvi goma daga cikinku ya ba ni mutum xaya daga mabiyansa. Ya ku mutanen Kufa, an jarrabe ni cikinku da ’ya’ya biyar tsinana; Kurame masu kunnuwa, bebaye masu zaqin baki, makafi masu idanun ganin gari, waxanda ke ba ’yan halal ba a wajen gamo (da abokan gaba), waxanda ke ba ’yan’uwa ba da za a amincewa lokacin musifa. Allah wadaranku! Ya masu kama da raquman da makiyayinsu ba ya nan; ko da yaushe ka tara su ta nann sai su watse ta can! – (Nahajul Balaga, 1/187).

Wannan shi ne halin mabiya Ali (R.A), wato ’yan Shi’a, kamar yadda shi da kansa ya fahimce su, kuma kamar yadda ya faxa musu a gabansu. Kuma wannan malamin Shi’a suka rawaito shi, suka kattaba shi a cikin littattafansu; ba qage ne wani ya yi musu ba. Mai karatu ya dubi irin siffofin da ya ba su kuma ya lura da yadda ya yi burin canjinsu da mabiyan Mu’awiya kamar yadda ake canjo sulai da kogo goma.

Dangantakarsu da Hassan bin Ali (R.A):
Dangantakar Hassan (R.A) da ’yan Shi’a mabiyansa ba ta da bambanci sosai da dangantakarsu da ubansa a gabanninsa. Bari mu ji daga bakin malaman Rafilawa da kansu. Wani babban malaminsu wanda ya shahara da taurin kai da ta’assubanci, mai suna Idris Alhusaini, ya ba mu labari dangane da haka. Ya ce: “Kuma Imam Hassan (A.S) ya fuskanci yunqurin kisan gila daga wasu bangare na dakarun rundunarsa. Wata rana wani mutum daga qabilar Banu Asad bin Sinan ya zabura ya kama akalar taguwarsa, kuma ya soki Imam xin a cinyarsa, sai Imam xin ya rumbace shi suka faxi qasa. Daga nan Abdullahi bin Hanzal Alxa’i ya kawo xauki, ya qwace makamin dga hannun mutumin ya soke shi da shi.” – (Duba littafin Laqad Shayya’anil Hussaini na Idris Alhussaini, bugun Darul Nakhil, Beirut, 1414BH, shafi na 279).

Wannan shaida, daga wannan malamin Shi’a xan hayaqi, tana nuna yadda a cikin rundunar Imam Hassan (R.A) ake da wani gungun mutane waxanda suke yaudararsa, suna yi masa zagon qasa, kuma suna neman dama ta kashe shi kisan gila. Waxannan mutane su ne suka kashe Ali (R.A) tun da farko, kuma su ne daga bisani suka kashe xansa Hussaini.

Wannan ya sa Hassan (R.A) ya riqa faxin kamar yadda shaihin Rafilawa Abu Mansur Alxabarsi ya rawaito: “Ina ganin wallahi Mu’awiyya ya fiye min waxannan. Suna riya cewa su magoya bayana ne, amma kuma sun nemi kashe ni, sun kwashe kayana, sun saci dukiyata. Wallahi in ba wa Mu’awiyya alqawari da zan tserar da raina da shi, in aminta cikin iyalina, ya fiye min ya kashe ni, iyalina su tagayyara. Domin idan na yaqi Mu’awiyya waxannan za su kama wuyana su miqa ni gare shi araha.” – (Duba Al’ihtjaj na Abu Mansur Ahmad bin Ali Aldabarsi, bugun Sharikul Kutubi, Beirut, 1414BH, 2/10).

Dangantakarsu da Hussaini bin Ali (R.A):
Wata qila daga cikin imaman Ahalul Baiti da shugabanninsu ba wanda ya cutu da mu’amalar ’yan Shi’a kamar Hussaini (R.A). Za mu qyale bayanin dangantakarsa da su sai a babi na gaba, inda za mu yi bayanin ta filla-filla.

Haka nan dangantakar ’yan Shi’a ta kasance da shugabannin Ahalul Baiti a tsawon zamani; yaudara da cuta da basarwa da zagon qasa. Idan ba su samu damar halaka wani Imami na Ahalul Baiti ba, to makamin qarya na nan. Za su laqa masa qarerayi iri-iri, su vata masa suna, su danganta masa bidi’o’i munana, kamar yadda suka yi ga Ja’afar Sadiq da ubansa Muhammad Baqir. Wannan ya sa aka rawaito Imam Musa Alkazim yana cewa: “Da zan bincika ’yan Shi’armu da ban same su ba face maqaryata. Da zan jarraba su da ban same su ba face masu ridda. Da zan tantance su da xaya ba zai sha ba cikin dubu.”

SHAHADAR HUSSAINI A KARBALA
Wannan ita ce dangantakar Rafilawa da waxanda suke da’awar cewa su shugabanninsu ne, kuma wannan irin dangantaka ita ce Hussaini (R.A) ya gada a lokacin da ya xauki ragamar shugabancin mabiyan ubansa a bayan rasuwarsa da rasuwar xan uwansa Hassan (R.A).

Bayan mutuwar Sarkin Musulmi Mu’awiya binu Abi Sufyan (RA) da hawan xansa Yazidu a kan karagar khalifa, vangarori da yawa ba su yi maraba da mulkin Yazidu ba saboda xarewarsa bisa karagar mulki ya sava tafarkin da Khalifofi Huxu Shiryatattu suka bi na rashin gadawa ‘ya’yansu ko makusantansu mulkin Musulmi. Banda wannan kuma, akwai da yawa daga ‘ya’yan Sahabbai waxanda suka fi shi cancanta, kamar Abdurrahman bin Abubakar da Abdullahi bin Umar da Hussaini bin Ali da Abdullahi bin Abbas da Abdullahi bin Zubair, da sauransu. Don haka an samu tawaye ga mulkin Yazidu a Hijaz (Makka da Madina) da Iraqi (Kufa da Basra). Kusan ba inda Yazidu ya samu goyon baya sosai sai a qasar Sham inda da ma nan ne fadar mulkin ubansa Mu’awiya. A yunqurin murqushe wannan tawaye munanan abubuwa na fitina sun faru waxanda babu shakka Yazidu ke xaukar alhakinsu. Babba daga cikin waxannan abubuwa shi ne mutuwar Hussaini.

Wasiqun Mutanen Kufa ga Hussaini:
Bayan xarewar Yazidu a kan karagar mulki da bayyanar qyamar mulkinsa daga ’ya’yan manyan sahabbai a Madina, mutanen Iraqi waxanda aka san su da goyon bayan Ali bin Abi Xalib da zuriyarsa, sun yi ta aike wa Hussaini da wasiqu, suna shaida masa cewa su sun haxa kansu kuma a shirye suke su yi masa mubaya’a kuma su taimake shi ya yaqi Yazidu matuqar dai ya fita zuwa wajensu a Kufa. Mutane da dama a Madina, ciki har da xan’uwansa Muhammad bin Ali (Binul Hanafiyya) da Abdullahi bin Abbas, sun shawarci Hussaini da kada ya fita zuwa Kufa, suna masu tuna masa yadda mutanen Iraqi suka yaudari ubansa Ali, suka nuna masa goyon baya sa’an nan daga bisani suka basar da shi a kashe shi a tsakaninsu. Wannan ya sa Hussaini (R.A) ya yi jinkirin fita.

Amma mutanen Kufa ba su qyale Hussaini ba; maimakon haka sun nace, suka yi ta aika masa da ruwan wasiqu, suna masu qarfafa masa gwiwa, suna yi masa alqawari da taimako da xa’a da biyayya. Bari mu saurari malaman Shi’a da kansu, su yi mana bayanin irin wannan naci na mutanen Kufa da yadda wasiqunsu suka yi ta zuwa Madina, wasu bayan wasu, duka domin qoqarin fito da Hussaini daga mahaifarsa da da’awar wai za a yi masa caffa a taimake shi ya yaqi Yazidu.

Malamin Shi’a na wannan zamani, Ahmad Rasim Nafis, ya ce: “Mutanen Kufa sun rubuta zuwa Hussaini (A.S) suna cewa: “Ba mu da wani shugaba, don haka sai ka taho wataqila Allah ya haxa kanmu a dalikinka bisa bin gaskiya.” Wasiqu suka yi ta zuwa masa, xauke da sa hannu, suna kiran sa ya zo ya karvi mubaya’a, ya shugabanci al’umma a gwagwarmayarta da xagutan Banu Umayya.” – (Duba littafin Ala Khutal Hussaini na Dr. Ahmad Rasim Nafis, Bugun Gadir, Beirut, 1418BH, shafi na 94.

Wani malamin nasu, shi ma daga cikin malamansu na zamani, mai suna Kazim Hamd Al’ihsa’i yana cewa: “Wasiqu suka riqa bibiyar juna zuwa ga Imam Hussaini (A.S) har ya cika buhuna biyu da su. Wasiqa ta qarshe da ta zo masa daga mutanen Kufa ita ce ta hannun Hani bin Hani Alsubai’i da Sa’id bin Abdillahi Alhanafi. Da ya buxe ta sai ga shi an rubuta a cikinta: Da sunan Allah, mai rahama, mai jinqai. Zuwa ga Hussaini xan Ali, daga ’yan Shi’arsa kuma ’yan Shi’ar ubansa Sarkin Musulmi. Bayan haka, lallai mutane suna tsumayin ka kuma ba su da karkata sai gare ka. Sai ka hanzarta ka hanzarto.”

Har yau, mashahurin malamin riwaya na Rafilawa, mai suna Abbas Alqummi, yana ba mu labarin wannan naci na mutanen Kufa, ya ce: “Wasiqu suka yi ta kwararowa, har wasiqu xari shida suka zo masa a rana guda, daga waxannan marasa alqawarin. Amma duk da haka shi yana taka-tsantsan, ba ya amsa musu. Har wasiqu dubu goma sha biyu suka taro a wajensa.” – (Duba littafin Ashura na Kazim Hamd Al’ihsa’i Annajafi, bugun Mu’assasatul Balag, Beirut, 1411BH, shafi na 85).

Aiken Muslim bin Aqil:
Wannan shi ne yadda Rafilawa na Kufa suka yi ta aiko wa Hussaini (R.A) takardu, suna roqonsa da ya fita zuwa gare su za su zama rundunarsa kuma su taimake shi ya yaqi mulkin zalunci na Yazidu. Da abin ya yi yawa, sai Hussaini ya aike abokin wasansa, wato xan wan ubansa wanda suke ’yan maza zar, Muslim bin Aqil, domin ya je ya gane masa gaskiyar abin da yake faruwa a Kufa.

Muslim ya isa Kufa kuma ya sauka a gidan Mukhtar bin Abi Ubaid Althaqafi, wanda yake fitaccen mai goyon bayan Ahalul Baiti ne a garin. A cikin wannan gida ne Muslim ya riqa saduwa da shugabannin Shi’a daban-daban a cikin asiri, yana karvar mubaya’arsu a maimakon Hussaini. Ya kwashe lokaci mai tsawo yana tafiyar da wannan mitin na sirri ba tare da gwamnan Kufa mai goyon bayan Yaziu ya sani ba. Wannan gwamnan, Nu’uman bin Bashir, wanda tun da farko Mu’awiya ne ya naxa shi, kuma Yazidu ya tabbatar da shi a kan muqaminsa, sahabi ne daga cikin Sahabban Annabi (S.A.W), Allah ya yarda da su, kuma ya shahara da sauqin hali da rashin son fitina. Wannan ya sa wasu malaman tarihi suke ganin cewa ba wai bai san da zaman Muslim bn Aqil ba ne a babban birnin jiharsa, amma ya kau da kai ne kawai ya qyale shi kamar yadda suka tabbatar da yawan mutanen da suka yi wa Muslim bin Aqil mubaya’a. Wani daga cikinsu mai suna Abdurrazaq Musawi Almuqrim yana faxi kamar haka. “Yan Shi’a suka tarbi Muslim a gidan Mukhtar, suka yi maraba da shi, kuma suka nuna masa xa’a da miqa wuya. Sun yi ta zuwa suna yi masa mubaya’a har sai da ya qirga mutum dubu goma sha takwas. A wata ruwaya aka ce mutum dubu ishirin da biyar, a wata kuma dubu arba’in. Daga nan sai Muslim ya aike wa Hussaini yana ba shi labari cewa mutanen Kufa sun haxu a kan yi masa biyayya uma suna jiran sa.” – (Duba Maqtalul Hussain na Abdurrazaq Musawi Almuqrim, Bugun Darul kitabail Islami, Beirut, 1399BH shafi na 147; da Ma’asat Ihda wa Sittin na Abdul Hassain (wai ma!) Nuruddin Al’amili, Bugun Darul Firdaus, Beirut, 1986, shafi na 24).

Wannan shi ne abin da ya faru kamar yadda wannan malami na ’yan Shi’a ya zayyana. Da Muslim bin Aqil, xan aiken Hussaini (R.A), ya ga yawan mutanen da suka ba shi mubaya’a, sai ya aike da saqo yana sanar da xan’uwansa da ya gaggauta ya taho Kufa domin mutanen garin ba su da wani shugaba sai shi.

Tafiyar Hussaini Zuwa Kufa:
A lokacin da waxannan abubuwa suke faruwa, Sarki Yazidu ya samu rahoton zuwan Muslim bin Aqil garin Kufa da kuma abin da ya faru na mubaya’a a gidan Mukhtar. Kuma ga alama ya ga sassaucin da gwamnansa, Nu’uman bin Bashir (R.A), ya nuna don haka bai yi wata-wata ba sai ya tuve shi. A makwafinsa ya naxa Ubaidullahi bin Ziyad kuma ya ba shi umarni da ya yi maganin abin da ya xauka a matsayin tawayen mutanen Kufa. Sabon gwamnan wanda shi ba sahabi ba ne kuma ga alama xan miya ta yi zaqi ne yana neman shiga a wajen Yazidu, bai wani vata lokaci ba sai ya kame Muslim bin Aqil ya kashe shi, sannan ya karkashe wasu shugabannin ’yan Shi’a, wasu kuma ya kame su ya tsare. Ganin haka, sai sauran shugabannin Rafilawa suka gudu, wasu kuma suka vuya. Kuma zancen an yi wa wakilin Hussaini mubaya’a ya mutu; babu ma mai son a haxa sunansa da Hussaini ko xan aikensa Hussaini wanda bai samu labarin abin da ya faru a Kufa ba, ya yi shiri ya fito daga Makka, inda ya je don aikin Hajji, kuma ba wanda ya taho tare da shi sai kaxan daga cikin danginsa da mutanen gidansa. Duk adadinsu mutum tamanin ne, ko da xoriya. Sai a kan hanya ne ya samu labarin kisan xan aikensa Muslim bin Aqil. Wannan labari da farko ya sa Hussaini ya yi nufin juyawa zuwa gida, amma sai ’ya’yan Muslim da ke tare da shi suka nace a kan cewa lallai sai an xauki fansar kisan mahaifinsu. Wannan ya sa Hussaini (R.A), ko da yaushe a yanzu alamu suna nuna yana tunkarar hatsari ne, amma duk da haka ya ci gaba da tafiyarsa zuwa Kufa.

Shi kuwa sabon gwamnan Kufa, Ubaidullahi bin Ziyad, a lokacin da ya ji labarin tahowar Hussaini sai ya tanadi runduna mai girma a qarqashin jagorancin Umar bin Sa’ad bin Abi Waqqas, ya aike su domin su tare Hussaini a kan hanya kuma su kama shi. Ya ba su umarni cewa idan suka riske shi su zo da shi a xaure cikin sarqa, idan kuma ya qi miqa wuya to su yaqe shi.


Mabiyan Hussaini Sun Basar da Shi:
Hussaini (R.A) ya ci gaba da tafiya, yana dosar Kufa, a lokacin da ya shiga qasar Iraqi maimakon ya haxu da masu taryensa, sai ya gamu da runduna ta mayaqa dubu ’yan gitta qarqashin Hurru bin Yazid waxanda suka yiwo gaba daga cikin rundunar Umar bin Sa’ad. Wannan runduna ba ta zo ne domin maraba da Hussaini ba, ko don ta tarve shi, amma ta zo da umarnin ta kama shi. Malamin Shi’a, Ali bin Musa bin Ja’afar bin Xawus Alhussaini, yana ba mu labarin yadda wannan kacivis ta kasance. Ya ce: “Hussaini ya yi ta tafiya har lokacin da ya isa marhala biyu (tafiyar wuni biyu) tsakaninsa da Kufa sai ya gamu da Hurru bin Yazid tare da mahaya dubu. Hussaini (A.S) ya ce masa: “Gare mu ko a kanmu?” (Hurru) ya ce: “A’a, a kanka dai, ya Abu Abdillahi”. Sai Hussaini ya ce: “La haula wala quwwata illa billahil aliyyil azim”. Sannan suka yi sa-in-sa har daga qarshe Hussaini (A.S) ya ce: “Idan a yanzu kuna kan savanin abin da wasiqunku suka zo mun da shi, ’yan aikenku suka sanar da ni, to sai in koma daga nda na fito”. Sai Hurru da rundunarsa suka hana masa wannan. Ya ce da shi: “A’a ya xan Ma’aikin Allah, ka xauki turbar da ba za ta kai ka Madina ba, kuma ba za ta kai ka Kufa ba, domin in yi uzuri ga (gwamna) bin Ziyad cewa mun yi savani a hanya. “Sai Hussaini ya xauki hanyar hagu, har ya isa (wani wuri da ake kira) Azibul Hajanat”. – (Duba Maqtalul Hussaini na Ali bin Musa bin Dawus Bugun Mu’asssatul A’alami, Beirut, 1414BH shafi na 47; kuma a duba Almajalisul Fakhira fi Ma’atimil Quddatil Dahira na Abdul Hussaini (wai ma!) Al’amil, bugun Mus’assasatul Wafa, Beirut ba tarihi, shafi na 87).

Wani malamin na Shi’a mai suna Ayatullahi Muhammad bin Taqiy Aali Bahril Ulum, yana ba mu labarin wannan gamuwa ta Hussaini (R.A) da rundunar ’yan gitta na Hurru bin Yazid, da yadda ya nemi su bar shi ya koma gida bayan ya sakankance da cewa mabiyansa sun basar da shi. Ya ce: “Hussaini ya yi wa rundunar jawabi, yana cewa: “Ni ban zo muku ba sai da wasiqunku suka je mun, ’yan aikenku suka isa gare ni suna cewa: Ka taho zuwa gare mu domin ba mu da shugaba; wata qila Allah ya haxa kanmu a dalilinka bisa shiriya. Idan kuna kan wannan abu da kuka faxi, to gani na zo, sai ku ba ni alqawari da zan nutsu da shi. Idan kuwa ba ku son zuwa na, to sai in koma ga barin ku zuwa wurin da na fito.” Sai suka yi shiru baki xayansu. Sannan aka yi kiran Sallar Azahar. Hussaini ya tambayi Hurru, “Za ka limanci mutanenka?”(Hurru) ya ce: “A’a za mu yi Salla gaba xaya a bayanka”. Sai Hussaini ya limance su. Sannan bayan ya idar da Salla, sai ya fuskance su, ya ce: “Ya ku mutane! Idan kuka tsoraci Allah, kuka ba wa masu haqqi haqqinsu, to wannan zia yardar da Allah. mu iyalin gidan Muhammad (S.A.W) mun fi cancanta da wannan al’amari daga waxancan masu da’awar abin da ba nasu ba. Idan kuma kuka qi mu, kuka jahilci haqqinmu, kuka sauya ra’ayi savanin abin da wasiqunku suka nuna, to sai in koma ga barin ku.” Sai Hurru ya ce: “Ni ban san wasiqun da kake faxi ba”. Sai Hussaini ya yi umarni aka fito masa da buhu biyu na wasiqu. Yayin da ya gansu, sai ya ce: “Ni ba na cikin waxanda suka aika ma da wasiqu. Kuma ni an ba ni umarni cewa idan na haxu da kai kada in qyale ka sai na kai ka Kufa gaban Bin Ziyad. Bayan musanyen yawu, sai Hurru ya ce: “Ka xauki hanya da ba ta zuwa Kufa, ba ta zuwa Madina don in rubuta wa Bin Ziyad (cewa mun yi savani).” – (Duba Waqi’atud Daffi na Muhammad Taqiy Aali Bahril Ulum, bugun Daruz Zahra, Beirut, 1412, Beirut 1412, BH 191-192).

Wannan shi ne karo na farko da Hussaini (R.A) ya tabbatar, ya ji da kunnuwansa kuma ya gani da idanunsa, cewa mabiyansa waxanda suka aike masa da dubunnan wasiqu suna gayyatarsa kuma suka ba wa xan aikensa mubaya’a kan xa’a da biyayya, sun basr da shi kuma sun warware alqawari. Don haka ya quduri aniyar komawa Madina amma wannan ma ba ta samu ba.

Wannan qissa kusan duk wanda ya yi rubutu a kan tahowar Hussaini zuwa Kufa daga cikin malaman Rafilawa ya tabbatar da ita. Daga malaman Shi’awa waxanda suka tabbatar da wannan qissa akwai Abbas Alqummi – (Duba littafinsa, Muntahal Aamal fi Tarikhin Nabiyyi wal Aal, bugun Addarul Islamiyya, Beirut, 1414BH, 1/464) da Abdurrazzaq Musawi Almuqrim – (Duba littafinsa, Maqtalul Hussain, bugun Daruk Kitabil Islami, Beirut 1399 BH, shafi na 183) da Baqir Sharif Alqurashi – (Duba littafinsa, Hayatul Imamil Hussain, Bugun Madarasatul Iriwani, Tehran, ba tarihi, 1/75) da Sharif Aljawahiri – (Duba littafinsa, Muthirul Ahzan, bugun Darul Kitabil Islami, Beirut ba tarihi, shafi na 43) da Asad Haidar – (Duba littafinsa, Ma’al Hussain fi Nahdatin, bugun Darut Ta’arul, Beirut, 1399 BH, shafi na 165) da wasunsu.

Daga abin da wannan qissa ta qunsa za mu fahimci cewa:
Hussaini (R.A) yana sa tsammanin gamuwa da ’yan tarba, ko da yake akwai shakku a zuciyarsa saboda labarin mutuwar Muslim bin Aqil, shi ya sa ya tambaye su, “Gare mu ko a kanmu?”.
Hurru da rundunarsa ’yan Shi’ar Hussaini ne amma a yanzu sun juya masa baya, saboda tsoron bonen gwamnan Kufa da kuma kwaxayin romonsa. Wannan ya sa Hurru ya kira shi da xan Ma’aikin Allah, ya yi Salla a bayansa, kuma ya nemi kuvutar da shi, ko da yake a lokacin guda shi ma yana son kuvutar da kansa, ta hanyar ba shi shawara da y a sauya hanya.
Hurru da rundunarsa sun san da aiken wasiqun ’yan Shi’a zuwa Hussaini shi ya sa da ya yi maganar wasiqu da ’yan aike da farko ba su musa ba; suka yi shiru. Sai daga baya ne suka samu qarfin gwiwar musawa.
Hussaini (R.A) ya ci gaba da kwaxayin juyo da hankalin mabiyansa zuwa gare shi, inda ya qara yi musu jawabi bayan idar da Salla, ya tuna musu da alqawarinsu, kuma ya nuna musu takardunsu. Amma ga alama tsoro da kwaxayi sun riga.
Haka nan mutanen Kufa mabiyan Hussaini, masu da’awar son Ahalul Baiti da jivintar su, suka juya wa Hussaini (R.A) baya saboda tsoro da kwaxayi, suka wayi gari suna yaqar sa maimakon taimakonsa, bari mu saurari malaman Rafilawa su da kansu mu ji abin da suke faxi dangane da wannan juyi mai ban mamaki. Hussaini Kurani, wani malaminsu da ya yi bincike a kan lamarin, yana cewa: “Mutanen Kufa ba su isu da watsewa ga barin Hussaini ba kawai, amma sun juye saboda sauyawar matsayinsu zuwa wani matsayi na uku, shi ne cewa sun fara gaggawar fitowa zuwa Karbala don yaqar Imam Hussaini (A.S), kuma a Karbala xin suna rige wajen cim ma abin da zai yardar da Shaixan ya fusata Allah (wato kowannensu yana qoqarin yin wani abu na kisan Hussaini ko tozarta shi da zai sa ya yi gwaninta wajen gwamnan Kufa). Ga misali, muna ganin Amru bin Hajjaj wanda a jiya ya fito yana nuna kansa a Kufa a matsayin mai kare mutuncin Ahlul Baiti, kuma ya jagoranci runduna domin ya ceci Hani bin Urwa, sai ga shi ya sauya wannan matsayi nasa, yana tuhumar Imam Hussaini da ficewa daga addini, yana cewa: “Ku yaqi wanda ya fice daga addini, ya rabu da jama’a”. – (Duba Fi Rihab Karbala na Hussaini Kurani, bugun Darut Ta’ruf, Beirut, 1413BH, shafi na 60 – 61).
Wato mai kare Hussaini a jiya, wanda ya jagoranci runduna don ya ceci mabiyan Hussaini da cewa ya zama xan tawaye, ya fice daga addini, ya rabu da jama’a. Dubi yadda munafincin ’yan Shi’a ya kasance da shaidar malaman Shi’a su da kansu.

Gamuwar Hussaini da Rundunar Umar:
Bayan Hussaini (R.A) ya karvi tayin Hurru da rundunarsa, inda ya saki hanyar Kufa ya karkace ya bi hagu, ya ci gaba da tafiya har ya isa wani wuri da ake kira Karbala. A nan ya sake yin kacivis da babbar rundunar da gwamnan Kufa Ubaidullahi bin Ziyad ya turo a qarqashin jagorancin Umar bin Sa’ad. Babu takamaimai yadda wannan runduna ta samu labarin hanyar da Hussaini ya xauka, har ta sha kansa. Tana yiwuwa akwai wasu ’yan rahoto waxanda suka kai labarinsa. Ala kulli halin, Hussaini (R.A) ya yi kacivis da wannan runduna mai mayaqa sama da dubu huxu kuma kwamandan wannan runduna ya neme shi da ya miqa wuya abin da shi kuma ya qiya.
Rundunonin guda biyu duka sun kafa sansani a Karbala, kuma tattaunawa mai tsawo ta gudana a tsakaninsu. Hussaini (R.A) ya nemi Umar bin Sa’ad ya bar shi ya koma gida Madina ko kuma ya qyale shi ya wuce kai tsaye ya gana da Yazidu a Birnin Dimashqa. Shi kuwa Umar bin Sa’ad ya nace sai lallai Hussaini ya miqa wuya a kai shi gaban gwamna Ubaidullahi a matsayin fursunan yaqi. Babu shakka akwai wulaqanci ga Hussaini (R.A) a cikin wannan matsayi da kwamandan ya xauka; domin matsayin Hussaini ya wuce ya tattauna da Ubaidullahi bin Ziyad, balle a ce ya je gabansa xaure cikin sarqa. Saboda haka ana iya cewa Hussaini ya nemi masalaha amma Umar bin Sa’ad ya nace kai da fata sai ya ci mutuncinsa. Wannan kuwa abu ne da mutuwa ta fi sauqi a kansa. Saboda haka Hussaini (R.A) ya xauki zavin yaqi duk da bambanci mai girma da ke tsakanin rundunarsa da ta abokan gabarsa.

Yadda Hussaini ya yi Shahada:
Yaqi ya kaure tsakanin rundunar Umar bin Sa’ad mai dakaru dubu huxu da ’yan rakiyar Hussaini (R.A) waxanda duka-duka ba su kai mutum xari xaya ba, kuma da yawa daga cikinsu mata ne da yara qanana. A gaskiya wannan ba a iya kiransa yaqi ta kowace fuska aka dube shi, amma kisan kiyashi ne kawai aka yi wa wannan babban bawan Allah shi da iyalinsa.
Malaman Shi’a suna jin daxin ba da labarin shahadar Hussaini (R.A) da irin jarumtar da ya nuna da matuqar wahalar da ya sha kafin y a gamu da ajalinsa da kuma yadda aka wulaqanta gawarsa bayan kashe shi. Suna yin wannan domin fusata jahilan mabiyansu da zuga su domin su sa qiyayya a zukatansu ga waxanda suke zargi da kisan Hussaini (R.A) a bisa qarya da zalunci, wato Ahalus Sunna. Mu a nan mun zavi mu kau da kai ga barin bayani filla-filla yadda Hussaini (R.A) ya yi shahada domin labari ne mai ban takaici wanda yake sa baqin ciki a zuciyar dukkan Musulmi.
Abin da kawai za mu ambata shi ne cewa, babu shakka Hussaini (R.A) ya nuna jarumta da sadaukantaka irin ta mahaifinsa Ali bin Abi Xalib (R.A), kuma ya yi yaqi irin yaqin mazaje masu imani da sharafi. Bayan kashe yawancin maza da ke cikin tawagarsa, waxanda suka haxa da ’ya’yansa da qannensa da ’ya’yan xan’uwansa Hassan (R.A) da ’ya’yan xan baffansa Aqil, da wasu masu yawa daga iyalin gidan Annabi (S.A.W) Ahalul Baiti, Hussaini (R.A) ya kare kansa, ya fuskanci wannan runduna shi kaxai, inda ya yi ta karawa da su har ya gamu da abin da Allah ya rubuta masa na shahada da samun karamar duniya da lahira. Su kuwa waxanda suka kashe shi sun yi asara duniya da lahira, kuma qasqanci da la’ana sun bi su har abada.

Wane ne ya Kashe Hussaini (R.A)?
Bayan mai karatu ya ga yadda al’amura suka wakana tun daga fitowar Hussaini (R.A) daga Makka har zuwa gamuwa da ajalinsa a Karbala, kuma a duk abin da muka kawo na ruwaya mun dogara da naqalin malaman Shi’a, to bari a yanzu mu yi qoqarin amsa wannan tambaya da harshen Ahalul Baiti su da kansu, kuma har yau ta hanyar ruwayar malaman Rafilawa da suka tabbatar a cikin littattafansu. Shaihunan Shi’awa sun ruwaito cewa: “Lokacin da aka shigo da iyalin Hussaini (R.A) garin Kufa a matsayin ribatattun yaqi, bayan kashe ubansu Hussaini (R.A), xansa Ali bin Hussaini (Zainul Abidin) ya faxa wa mutanen Kufa kamar haka: “Ya ku mutane! Ina gam muku da Allah, ko kun sani cewa kun aike wa mahaifina wasiqu, kuka yaudare shi, kuka ba shi alqawari da mubaya’a sannan kuka bashe shi, kuka kashe shi? Wadaranku, wadaran abin da kuka gabatar wa da kawunanku. Da wane ido za ku dubi Manzon Allah (S.A.W) lokacin da zai ce muku: Kun kashe zuriyata, kun keta alfarmata, saboda haka baku cikin al’ummata!
“Sai muryoyin mata suka ruxe da kuka, kuma mutanen suka ce da junansu: “Kun halaka ba ku sani ba”. Sai shi (A.S) ya ce: “Allah ya yi rahama ga mutumin da ya karvi nasihata, ya kiyaye wasiyata dangane da Allah da ManzonSa da mutanen gidansa. Lallai muna da abin koyi mai kyau ga Manzon Allah. sai dukkaninsu suka ce: “Mu dukkaninmu masu ji ne gare ka, masu biyayya ne, masu kiyaye alqawarinka ne, ba mu gudun ka. Ka umarce mu da umarninka, Allah ya rahamshe ka, za mu yi yaqi da yaqinka, kuma za mu yi sulhu da sulhunka. Za mu kama Yazidu (a hannu), mu barranta daga wanda ya zalunce ka ya zalunce mu”. Sai shi (R.A) ya ce: “Ina! Ya ku mayaudara makirai! An shiga tsakaninku da son zukatanku. Kuna nufin ku yi min irin abin da kuka yi wa iyayena tun da farko? A’a, na rantse da Allah! raunina har yau bai warke ba. An kashe ubana jiya tare da mutanen gidansa, kuma rashin Manzon Allah (S.A.W) da rashin ubana da ’yan’uwana bai huce ba. Baqin cikinsu da xacinsu yana nan a maqoshina. Kuma xacin gunarsu yana qirjina”.
Wannan huxuba ta Ali Zainul Abidin (R.A) manyan marubutan Shi’a sun kattaba ta a cikin littattafansu. Daga cikinsu akwai Ahmad bin Ali Axxabarsi – (Duba littafinsa, Al’ihtijal, bugun Sharikatut Kutubi, Beirut 1414BH, shafi 2/32). Da Muhsin Amin Al’amili –(Duba littafinsa, Lawa’ijul Ashjan, bugun Darul Amir, Beirut 1996, shafi na 158). Da Abbas Alqummi – (Duba littafinsa, Muntahal Aamal fi Tarikh Annabiy wal Aal, bugun Addarul Islamiyya, Beirut 1414BH 1/572). Da Hussaini Kurani – (Duba littafinsa, Fi Rihab Karbala, bugun Darut Ta’aruf, Beirut 1413BH, shafi na 183). Da Rida Alqazwini – (Duba littafinsa, Tazallumuz Zahra, bai gidan bugu, Beirut ba tarihi, shafi na 262). Da wasu masu yawa ban da waxannan. Kamar yadda mai karatu ya sani, bayan Hussaini (R.A) a duk zuriyar Ahalul Baiti babu wani kamar xansa Ali Zainul Abidin. To wannan ita ce shaidarsa dangane da waxanda suka kashe ubansa. Wato Ahalul Baiti suna xauka cewa mabiyansu, masu da’awar jivintar su da yi musu biyayya, su ne waxanda suka yaudare su, suka ci amanarsu, suka basar da su, kuma wannan munafinci nasu shi ne sanadin mutuwar Hussaini (R.A).
Domin qara tabbatar da wannan, ga shaidar Ummu Kulsum ’yar Ali (matar Umar bin Khaxxab) wacce take tana tare da xan’uwanta shaqiqinta Hussaini a lokacin da ya yi shahada. An ruwaito tana cewa, kamar yadda mashahurin malamin Shi’a, Muhsin Amin Al’amili ya ruuta: “Ya mutanen Kufa! Me y a same ku kuka basr da Hussaini, kuka kashe shi? Sannan kuka yashe dukiyarsa kuka gaje shi? Kuma kuka ribace matansakuka tozarta shi? To Allah wadaran ku! Allah ya nesanta ku! Wacce irin musifa kuka jawo wa kanku, wane irin nauyi kuka xauka a kan bayanku, wane irin jini kuka zubar? Kun kashe mafificin mutane bayan Annabi (S.A.W) kuma an xebe rahama daga zukatanku.”
A wata ruwayar aka ce Ummu Kulsum ta leqo da kanta adga haudajin da ke xauke da ita, a lokacin da aka shigo da ita birnin Kufa mutane suka tare da da kuka, ta ce: “Ku rufe mana baki, ya ku mutanen Kufa, ya mazanku za su kashe mu sannan matanku su yi mana kuka?! Mai hukunci tsakaninmu da ku shi ne Allah ranar alqiyama”. – (Duba Lawa’ijul Ashjani na Muhsin Amin Al’amili bugun Darul Amir, Beirut, 1996, shafi na 157).
Wannan ita ce shaidar shugabannin Ahalul Baiti dangane da waye ya kashe Hussaini (R.A) kuma daga ruwayar marubutan Shi’a su da kansu. Amma malaman Shi’a masu ha’inci da yaudara suna laqa wannan qazamin aiki ga Ahalus Sunna a kan qarya da zalunci domin su saka gaba da qiyayya a zukatan jahilan mabiyansu waxanda a kullum suke zugawa da su xauki fansar kisan Hussaini (R.A) a kan Ahalus Sunna waxanda ba su ji ba, ba su gani ba.

Ha’incin Malaman Shi’a:
Yana daga cikin ha’incin malaman Shi’a yadda suke voye tarihin wasu daga cikin iyalin Hussaini, Ahalul Baiti, waxanda suka yi shahara tare da shi a Karbala saboda suna xauke da sunayen manyan Sahabbai. Suna yin wannan ne kuma domin su voye yadda shugabannin Ahalul Baiti suka sanya wa ’ya’yansu sunayen manyan Sahabbai kamar Abubakar, Umar, Usman, Abdurrahaman, Aisha, da sauransu, domin qauna da soyyaya da suke musu kuma dan neman albarkarsu. Anan za mu ambata sunayen manyan zuri’ar Ahlul Baiti waxanda suke xauk da sunayen manyan sahabbai kuma waxanda suke sun yi shahada sa Hussaini (RA) a karbala tare da ambaton wasu daga cikin malaman Shi’a waxanda suka hakaito sunayensu a cikin littafansu.

Abubakar binu Ali binu Abi Xalin. Daga cikin malam shi’a da suka ambace shi akwai Muhammad binu Nu’uman Almufid da Abbas Alqummi da Baqir Sharif Alqurashi da Sadiq Makki da ibnu Shahar Aashur da wasu masu yawa banda waxannan.
Umar binu Ali binu Abi Xalib. Malaman shi’a da dama sun ambace shi, ciki har da Muhammad binu Nu’uman Almufid da ibnu Shahar Aashur sa kuma Hadi Annajafi.
Usman binu Ali Abi Xalib. Shi ma malaman shi’a sun ambace shi kamar su Binu N’uman Almufid da Abbas Alqummi da ibnu Shahar Aashur da Baqir Shaif Aqurashi da Hadi Annajafi da kuma Sadiq Makki.
Abubakar binul Hassan binu Ali binu Abi Xalib. Shi ma ya yi shahada tare da Hussaini(RA) a Karbala. Daga cikin waxanda suka shaida da haka har da mlalamn shi’a irin su Binu Nu’uman Almufid da Abbas Alqummi da Alqurashi da Annajafi da Sadiq Makki da wasunsu.
Umar binul Hassan binu Ali Abi Xalib. Waxannan marubutan shi’a sun ambace shi: Binu Nu’uman Almufid da Sadiq Makki.

Mun kawo waxannan sunaye ne a mastayin misali na yadda malaman shi’a, musamman na wannan qasar, suke ma mabiyabsu rufa-ido don sun san jahilcinsu da rashin tsinkayensu a cikin littafan qungiya da suke da’awar su mabiyanta ne. Idan da ‘yan shi’a, waxanda suke makafi ne duxum,n sun san cewa shugabannin Ahalul Baiti kamar Ali da Hassan da Husaini, Allah ya qara musu yarda, sun sanya ma;ya’yansu sunayen Abubakar da Umar da Usmanu ai da aqalla sa yi tambaya su ce me ya sa haka?! To amma da yake abin duhu ne ke dukan duhu, sai malaman Rafilawa su ci gaba da voye wannan haqiqa wacce take ga ta quru-quru a cikin littafansu, suna ha’intar Allah da Manzonsa kuma suna cin amanar ilimi. Sa’an nan alokaci guda suna ci gaba da zuga mabiyansu, masu vatan vakatantan, suna sa musu qiyayyar manyan bayin Allah a cikin zukatansu, suna yaxa gaba da qiyayya da fitina a tsakanin Musulmi. Muna roqon Allah da ya raba mu da jahilci kuma ya fisshe mu vata ga addini.

Matsayin Ahlul Sunna A Kan Kisan Husaini

Babu Shakka kisan Hussaini (RA) na daga cikin manyan musibu da suka tava afkawa wannan al’umma a tsawon tarihinta, wanda babu abinda Musulmi zai yi dangane da haka sai dai ya ce: Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un!

Malaman shi’a suna qoqarin xorewa Ahluls sunna alhakin wannan ta’asa, imma ta hanyar cewa su ne suka aikata wannan aika-aika saboda sarkin da abin ya faru a qarqashin mulkinsa sarkinsu ne sun yarda da shugabancinsa, ko kuma alal aqalli sin yarda da kisan kuma ba su ganin bekensa. Babu tantama wannan qarya ce wacce Allah ya barrantar da Ahlus Suna daga sharrinta.

Matsayin Ahlus Sunna dangane da kisan Hussaini(RA) matsayi ne wanda aka gina shi a kan ilmi da adalci, kamar yadda Allah ya yi umarni da haka. Ba sa kambama abin har su wuce da shi matsayinsa, kuma ba sa wulaqanta shi, su yi sako-sako da shi, ko su yi masa riqon sakainar kashi. Ga misali, koda yake suna xaukar kisan Hussaini a matsayin babbar musiba, to amma suna ganin kisan uban Ali binu Abi Xalib(RA) ya fi shi zama musiba; domin Ali yana gaba da Hussaini a musulunci nesa ba kusa ba. Haka nan, an kashe Umar binul Khaxxabi da Usmanu binu Affan waxanda su ma suna gaba da Hussaini a musulunci. Saboda haka, koda yake kisan Hussaini(RA) musiba ce babba, amma ba wata musiba ce wacce ba’a tava ganin irin ta ba a tarihin al’umma. A haqiqa, an ga wacce ta fi ta.

Shaihul Islami Ibnu Taimiya ya taqaice wannan matsayi na ilimi da adalci inda yake cewa, “Kuma lallai Allah ya grmama shi (Hussaini) da shahada kuma ya wulaqanta waxanda suka yarda da kisansa. Kuma yana da abin koyi kyakyawa da waxanda suka gabace shi na shahidai. Domin shi da xan uwansa (watau Hassan) su ne shugabanin samarin aljanna, kuma ga shi an raine su cikin xaukakar musulunci; ba su samu darajar hijira da jihadi da haquri a kan cuta ba kamar yadda sauran mutanen gidansu suka samu. Don haka sai Allah ya girmama su da shahada domin ya cikashe musu girmansu kuma ya xaukaki darajojinsu. Kuma lallai kisansa musiba ce babba. Allah Mai girma da Xaukaka kuwa ya shar’anta istirja’i a yayin musifa da faxinsa: “Kuma ka yi bushara ga masu haquri. Waxanda suke idan wata musifa ta same su, sai su ce; Lallai ne mu ga Allah muke, kuma lallai ne mu zuwa gare Shi masu komawa ne.” waxannan akwai albarku a kansu daga Ubangijinsu da wata rahama. Kuma waxannan su ne shiryayyu.” (Suratul Baqara: 155 – 157). – (Duba Majmu’ul Fatawa na Ibnu Tamiyya, 4/511).
Zaluncin Yazidu ga Al’umma
Ko da yake Yazidu Sarki ne na Daular Musulunci, kuma Ahalus Sunna sun yarda da mulkinsa, amma ba a kan son ransu suka yarda da shi ba, sai dai sun yarda da shi ne bisa dole don gudun fitina irin wacce ta faru har ta kai ga kisan Hussaini (R.A).
Ya tabbata a tarihi cewa lokacin da Mu’awiya ya yi nufin naxa xansa Yazidu a matsayin Yarima wanda zai gaje shi bayan mutuwarsa ya aike Madina don neman yardar Sahabbai waxanda suka rage da kuma ’ya’yan manyan Sahabbai da ke zaune a wannan gari. A wannan lokaci akwai Abdullahi bin Umar da Hussaini bin Ali da Abdurrahman bin Abibakar da Abdullahi bin Zubair. Dukkaninsu ba su goyi bayan wannan nufi na Mu’awiyya ba. Don haka sai Mu’awiyya ya tafi da kansa inda ya iske su a Makka (sun gudu zuwa Makka a lokacin da suka qi ba wa gwamnan Mu’awiyya mubaya’ar Yazidu a Madina). Bayan ya yi umra, Mu’awiyya ya kira waxannan shugabanni na Musulmi kuma ya tilasta musu yin mubaya’a ga xansu Yazidu, kuma sun yi mubaya’ar a kan tilas don tsoron rayukansu da gudun fitina ga Musulmi. – (Duba Albidaya wan Nihaya na Isma’il bin Kathir, bugun Beirut, 1974, 8/79; da Alkamil fit Tarikh na ibnul Athir, bugun Beirut, 1385/1965, 3/510).
Don haka lokacin da Mu’awiyya ya rasu, kuma xansa Yazidu ya xare bisa karagar mulki, Madina a matsayinta na babbar matattarar shugabannin Musulmi ta zama cibiya ta adawa da mulkin sabon Sarki Yazidu.
Wannan ya sa Sarki Yazidu ya sake neman shugabanni a Madina da su sabunta masa mubaya’a, wato su yi masa caffa don tabbatar da yardarsu da mulkinsa da biyayyarsu gare shi. Amma sai waxannan shugabanni suka qi.

Yaqin Madina (Hirra)
Labari ya watsu na adawar mutanen Madina ga mulkin Yazidu sai mutane daga ko ina a Daular Musulunci suka goyi bayan matsayin mutanen Madina kuma adawa da mulkin Yazidu ta yi tsanani. A daidai wannan lokaci ne wasiqun mutanen Kufa suka fara zuwa ga Hussaini (R.A) suna kira da ya fita zuwa gare su domin su yi masa caffa ya yaqi Yazidu. Hussaini ya amsa kiran mutanen Kufa kuma ya fita zuwa wajensu, kuma abin da ya faru ya faru na kisan kiyashin Karbala da shahadar Hussaini (R.A) kamar yadda bayani ya gabata.
Bayan shahadar Hussaini a Karbala, mutanen Madina sun yi tawaye ga mulkin Yazidu, suka kori gwamnansa, Usman bin Muhammad bin Abi Sufyan, suka naxa Abdullahi bin Hanzalata a makwafinsa. Abdullahi bin Hanzalata Ba’ansare ne, mahaifinsa shi ne mashahurin sahabin nan, Hanzalatu bin Abi Aamir, wanda ake wa laqabi da Algasil (wato wanda mala’iku suka wanke shi bayan ya yi shahada da janaba a jikinsa). Kuma shi ne ya jagoranci mutanen Madina a yaqin Hirra da suka gwabza da rundunar Yazidu ta mutanen Sham. Tawayen mutanen Madina ga Yazidu ya faru a shekara ta 62 bayan hijira, shekaru biyu bayan hawan mulkinsa kuma shekara guda bayan shahadar Hussaini.
Lokacin da Sarki Yazidu ya samu labarin tawayen mutanen Madina, ya tanadi runduna babba ya naxa Muslim bin Uqba ya shugabance ta. Shi Muslim bin Uqba ya shahara da tsanani da taurin rai da qeqashewar zuciya. Yazidu ya ba shi umarni da ya kira mutanen Madina zuwa ga yi masa xa’a, in kuma sun qi ya yaqe su. Sannan ya umarce shi da cewa idan ya yi nasara a kansu to ya halasta Madina kwana uku. Kuma haka abin ya faru. Muslim bin Uqba ya isa Madina a qarshen watan Zulhijja, shekara ta 63 bayan hijira. Ya yaqi mutanen Madina, bayan sun qi su yi caffa ga Yazidu, kuma wannan yaqi ya zama daga cikin mafi muni a tarihin Musulunci.
Bayan da rundunar mutanen Sham ta yi nasara a kan mutanen Madina, kwamanda Muslim bin Uqba ya halasta birnin, kamar yadda Yazidu y a umarce shi, inda dakarunsa suka kwashe kwanaki uku suna kisa, suna xibar ganima, suna qone dukiya, kuma suna fyaxe ga mata. Sun yi ta’addanci da ta’asa da xanyen aiki wanda a sakamakonsa xaruruwan ’ya’yan sahabbai, da dubunnan Musulmi na gari Ahalus Sunna, suka rasa rayukansu. Sun keta alfarmar garin Manzon Allah (S.A.W), sun ci mutuncin matan Musulmi, kuma sun yi xanyun ayyuka waxanda ko maguzawa sai haka. Ibn Kathir ya qiyasta yawan waxanda suka mutu a yaqin ya ce: “Waxanda suka mutu a yaqin Hirra mutum xari bakwai ne daga shugabannin mutane, Quraishawa da Ansarawa da Muhajirun da zavavvun ’yantattun bayi (na sahabbai). Kuma mutum dubu goma sun mutu na gama-garin mutane waxanda ba a san su ba, maza da mata, ’ya’ya da bayi. Har yau, Ibn Kathir ya qiyasta yawan matan da aka yi wa fyace ya ce: “Matan Madina dubu ne suka haihu ba miji bayan yaqin Hirra”.
Duba ka gani, mai karatu, zaluncin Yazidu da xanyen aikinsa da yadda ya zubar da jinin Musulmi Ahalus Sunna, sannan ka dubi zaluncin ’yan Shi’a inda suke dangana wannan azzalumin sarki ga Ahalus Sunna, suna nuna cewa wai shi shugabansu ne, saboda haka dole su xauki alhakin xanyun ayyukansa da tavargazozinsa, kamar kisan Hussaini!

Yaqin Makka:
Xanyen aikin rundunar Muslim bin Uqba bai tsaya a kan mutanen Madina ba kawai, amma ya wuce zuwa Makka inda ya yaqi mutanenta kamar yadda mai gidansa Yazidu ya umarce shi. Bayan kisan Hussaini (R.A) Abdullahi bin Zubair shi ya rage a cikin ’ya’yan Sahabbai wanda Yazidu yake shakkar sa. Ubansa shi ne Zubair bin Awwam, babban sahabi, xaya daga cikin sahabbai goma da Annabi (S.A.W) ya yi musu albishir da aljanna, kuma mahaifiyarsa ita ce Asma’u xiyar Abubakar, ’yar’uwar Innar Muminai Aisha (R.A). Don haka yana da qima a idanun Musulmi kuma ga alama, yana da babban buri na siyasa. Wannan ya sa Yazidu yake shayin sa. Bayan da mutanen Madina suka yi tawaye ga Yazidu, shi Abdullahi bin Zubair ya gudu zuwa Makka inda ya fake da alfarmarta, kuma mutane suka yi masa caffa yadda ya zama tamkar ya yanke qasar Hijaz duka daga mulkin Yazidu. Wannan ya sa Yazidu ya yi umarni ga rundunar Muslim bin Uqba cewa idan sun gama da Madina su wuce zuwa Makka su yaqe ta.
Bayan tavargazar Madina, wannan runduna ta ’yan ta’adda ta wuce zuwa birnin Makka, inda suka yi wa garin qawanya, suka kewaye shi har tsawon kwana sittin da huxu. Kafin rundunar ta iso Makka kwamandanta Muslim bin Uqba ya mutu a kan hanya, sai wani da ake kira Bin Numair Assakuni ya gaje shi a shugabancin rundunar. Tsakanin tavargazar Madina da mutuwar bin Uqba ’yan kwanaki ne kawai. Allah ya gaggauta sakamako ga wannan xan ta’adda, inda ya kashe shi kwanaki kaxan bayan keta alfarmar Madina, kamar yadda Annabi (S.A.W) ya ba da labari da haka. Bukhari ya ruwaito a cikin sahihinsa cewa Manzon Allah (S.A.W) ya ce: “Babu wani da zai yi kaidi ga mutanen Madina face ya narke kamar yadda gishiri yake narkewa a ruwa.
A birnin Makka ma, rundunar mutanen Sham ta Yazidu, qarqashin shugabancin bin Numair Assakumi ta aikata miyagun ayyuka, ta yi tavargaza iri-iri, inda malaman tarihi suka ce dakarun wannan runduna sun jefi xakin Ka’aba da makamin manjaniq, kuma sun yi sanadin qonewar wani sashe nata. Mutane da dama zavavvun Musulmi da ’ya’yan sahabbai, ciki har da Abdullahi bin Zubair, sun rasa rayukansu a wannan yaqi. Amma kafin yaqin ya qare, sai labarin mutuwar Yazidu ya iso Makka. Shi ma Allah ya gaggauta yi masa uquba sakamakon miyagun ayyukansa. Tsakanin mutuwarsa da tavargazar Madina wata uku ne kawai.
Ban da tavargazar Madina (yaqin Hirra) da yaqin Makka da kuma kisan Hussaini (idan ya tabbata da umarninsa ne ko yardarsa), akwai abubuwan assha da dama da aka danganta ga Yazidu waxanda ba za mu vata lokaci ba da ambatonsu a nan, saboda yin haka ba shi ne manufarmu ba a wannan littafi. Ko su waxannan yaqoqa guda biyu mun ambace su ne a dunqule domin mu tabbatar wa da mai karatu cewa Yazidu ba gwanin kowa ba ne. Shi ba shugaba ne na Ahalus Sunna wanda suke jivintarsa, suna goyon bayansa. Da a ce kisan Hussaini (R.A) laifi ne da Yazidu ya yi wa ’yan Shi’a, da sai mu ce laifin da ya yi wa Ahalus Sunna na yaqar Makka da Madina da kashe xaruruwan ’ya’yan Sahabbai ya ninka wanda ya yi wa Rafilawa ninki mai yawa. To ina ga cewa kisan Hussaini (R.A) shi ma Ahalus Sunna aka yi ma; domin Hussaini shugaba ne na Ahalus Sunna kamar yadda Abubakar da Umar, da sauran Sahabbai, Allah ya qara musu yarda, suke shugabanni a gare su. Don haka idan akwai waxanda Yazidu ya zalunta a haqiqa su ne Ahalus Sunna. To sai dai su Ahalus Sunna ba sa aiki da jahilci, kuma ba sa rama zalunci da zalunci irin sa. Wannan ya sa suke faxin abin da suka tabbatar dangane da Yazidu, abin da kuma suke da shakka, ko ba a iya tabbatar da shi, suke barin saninsa da hukuncinsa ga Allah. kuma a kan haka suka gina ra’ayinsu dangane da matsayin Yazidu.
Matsayin Yazidu a Wajen Al’umma
Yawancin malaman Sunna sun haxu a kan cewa Yazidu fasiqi ne. akwai wasu malamai da suka sava da wannan ra’ayi, kamar Abubakar ibnul Arabi, sai dai a haqiqa waxannan ba su da yawa.
Amma sun yi savani wajen kafirta shi. Wasu suka ce ya kafirta, daga masu wannan ra’ayi akwai shugaban mazhabar Hanbaliyya a zamaninsa, wato Imamu ibn Aqil, wanda ya rasu a shekara ta 513 bayan hijira da mashahurin malamin Tafsirin nan, Mahmud Aalusi. Hujjar masu wannan ra’ayi ita ce xanyun ayyukansa, kamar kisan Hussaini (R.A) da yaqar Madina da Makka da keta alfarmar waxannan birane biyu masu tsarki, da karkashe dubunnan Musulmi waxanda suka haxa da ’ya’yan manyan sahabbai da zavavvun magabata.
Wasu malamai kuma suka ce a’a, bai kafirta ba. Kuma wannan shi ne ra’ayin mafi yawan malaman Sunna. Hujjar masu wannan ra’ayi ita ce cewa dalilan da suke sa wa a yi hukunci a kan wan musulmi da cewa ya yi ridda ba su tabbata ba a kan Yazidu ta fuksar yaqini; don haka sai a bar shi a kan asali na kasancewar sa musulmi.
Haka nan, malamai sun yi savani dangane da halascin la’antarsa. Wasu suka ce ya halasta. Daga cikinsu akwai Imam Ahmad bin Hanbal da Alqali Abu Ya’ala (daga mazhabar Hanbaliya) da ibnul Jauzi (shi ma Bahanbale ne) da Ali bin Muhammad bin Ali Alxabari Alkayaharasi (daga mazhabar Shafi’iyya) da Attaftazani (daga mazhabar Hanafiyya) da wasunsu.
Wasu kuma suka ce su ba sa qaunar sa, amma ba za su la’ance shi ba. Wannan kuma shi ne ra’ayin mafi yawan malamai, ciki har da Hujjatul Islam Algazali da Shaihul Islam ibn Taimiyya da ibn Hajar Alhaitumi da sauransu. Dalilin Gazali da ibn Hajar shi ne cewa sam Yazidu bai yi umarni da kisan Hussaini ba. Shi kuwa ibn Taimiyya cewa ya yi ba ya halasta a la’ance shi sai idan ya tabbata cewa shi yana cikin fasiqai azzalumai waxanda ya halatta a la’ance su, kuma ya mutu a kan haka bai tuba ba.
Waxannan a taqaice su ne ra’ayoyin malamai dangane da matsayin Yazidu. Muna ganin babu shakka ra’ayin mafi yawan malamai shi ne ya fi waraka da kuvuta. Babu shakka miyagun abubuwa da xanyun ayyuka sun faru a zamanin Yazidu, amma sanin takamaimai, kuma filla-filla, yadda waxannan abubuwa suka faru yana da wuya saboda nisan zamani da bambancin ruwayoyi da hikayoyi na haqiqanin abin da ya faru, da kuma yadda ya faru. Don haka ana iya qin Yazidu saboda a dunqule kowa ya san waxannan abubuwa sun faru a zamaninsa, kuma a qarqashin mulkinsa, kuma dole ya xauki alhakinsu. Amma kasancewar haqiqanin hannunsa a ciki, ko umarninsa a kai, ko saninsa da yardarsa, to waxannan abubuwa ne waxanda sanin su ta fuskar yaqini sai Allah shi kaxai. Saboda haka yi wa mutum hukunci a kansu, tun da yake bai zama lallai ba, to sai mai hankali ya shafa wa kansa lafiya, kuma ya gode Allah da bai wuce xan kallo ba a cikin lamarin.
Kuma kamar yadda muke ganin ba za a yi wa Yazidu hukunci ba, muna ganin cewa babu mai son Yazidu, ko ya goyi bayansa, ko ya yabe shi, sai jahili wanda ya kai matuqa a jahilci, ko kuma munafuki wanda yake farin ciki da kisan zuriyar Annabi (S.A.W) da mabiyansa.

Maganganun Malamai Dangane da Yazidu:
A wannan vangare zan kawo maganganu da wasu malaman Sunna suka yi dangane da Yazidu don mai karatu y a san cewa babu wani mai bin tafarkin Sunna da ake izna da maganarsa wanda yake son Yazidu, ko yake yabonsa, ko yake goyon bayansa, savanin abin da ma’abota jahilci suke yaxawa.

Imam Ibnul Jauzi:
Mashahurin malamin mazhabar Hanbaliyya, Abdurrahman bin Ali bin Muhammad Albakari, wanda ya shahara da ibnul Jauzi wanda kuma yake mayar da nasabarsa ga Abubakar Siddiq (R.A), yana cewa: “Yana daga cikin qudurce-qudurcen gama-garin mutane masu danganta kansu ga Sunna cewa Yazidu yana kan sawaba kuma wai Hussaini (R.A) ne ya yi kuskure da ya yi masa tawaye… A haqiqa babu mai faxin haka sai jahili, mara basira, wanda yake zaton yana fusata Rafilawa (da maganarsa).

Umar bin Abdul-Aziz:
An ruwaito cewa, Halifan Banu Umayya mai adalci, Umar bin Abdul-Aziz, Allah ya yi masa rahama, ya kasance yana yin bulala ashirin ga duk wanda ya kira Yazidu da laqabin “Sarkin Musulmi”.
To sai mai karatu ya dubi wanna, kuma ya ga irin adalcin malaman Sunna. Sarkin Musulmi Umar bin Abdul-Aziz xan qabilar Banu Umayya ne, kuma Yazidu yaka cikin kakanninsa, amma da yake malami ne, kuma ya sha daga tafkin Sunna mai garxi, ka ji yadda ya xauki magabacinsa, Yazidu. Ana iya tunawa cewa, a cikin sarakan Banu Umayyad kaf, in ban da Mu’awiyya, ba a yi kamar Umar bin Abdul-Aziz ba, wanda jikan Umar bin Khaxxab ne ta wajen mahaifiyarsa.

Imam Ahmad bin Hanbal:
Salih bin Ahmad bin Hanbal ya ce: “Na ce da Babana, wasu mutane suna danganta mu ga jivintar Yazidu. Sai ya ce: “Ya kai xana, akwai mutumin da zai jivinci Yazidu matuqar dai ya yi imani da Allah?” Sai na ce: To me ya sa ba ka la’antar sa? Sai ya ce: Yaushe ka ga ina la’antar wani abu? Amma mai zai hana a la’anci wanda Allah ya la’ance shi a cikin littafinsa? Na ce: A ina Allah ya la’anci Yazidu a cikin littafinsa? Sai ya karanta: ‘To shin kuna fatan idan kun juya (daga umarnin) za ku yi varna a cikin qasa, kuma ku yanyanke zumuntarku? Waxannan su ne waxanda Allah ya la’ane su, sannan ya kurumtar da su, kuma ya makantar da ganinsu”. (Suratu Muhammad: 22 – 23). Sannan ya ce: “Akwai wata varna da ta fi kisa?”

Imam Azzahabi:
Muhammad bin Ahmad bin Usman Azzahabi, da yake lasafta masu ruwaya adalai, ya ce dangane da Yazidu, shi ba adali ba ne; ba ya cancanta a karvi ruwaya daga gare shi. Imam Ahmad ya ce bai cancanta a karvi ruwayarsa ba”.

Muhammad Rashid Rida:
Rashid Rida, wanda yana cikin manyan malaman Sunna na wannan zamani, wanda kuma wasu suke lasafta shi cikin mujaddadai, yana cewa: “Yana cikin wannan tawayen Imam Hussaini jikan Manzon Allah (S.A.W) a kan shugaban zalunci da qetare haddi, Yazidu bin Mu’awiyya, Allah ya wadaran sa, ya wadaran masu mara masa daga ’yan qungiyar Karramiyya da Nasibawa.”
Bukukuwan Ashura
Bayan ’yan Shi’a sun yi sanadiyyar kisan wanda suke da’awar cewa shi shugabansu ne, wato Imam Hussaini (R.A), ta hanyar tattago shi daga garinsu inda yake zaune cikin aminci da girma da karramawa, suka kawo shi tsakiyar abokan gabansa, sannan suka watse suka bar shi aka kashe shi, sai kuma suka qirqiro da wasu bukukuwa na zaman makokinsa da tunawa da shi.
Waxannan bukukuwa ana yin su ne galibi a ranar Ashura, wato goma ga watan Muharram, wacce ita ce ranar da Hussaini ya yi shahada. Bukukuwan sun haxa da ayyukan jahilci da sakarci kamar koke-koke da hayagaga; yin ihu da kururuwa da kiran na-shiga-uku; keta tufafi da cisgar gashi; marin kumatu da dukan qirji; da kuma dukan baya da wata qaramar majaujawa xaure sa sarqa har sai jini ya fita. Akwai kuma wani abu da suke kira TAXBIR inda maza suke aske kawunansu qwal-kwabo, sannan sai a sa wani xan buda a doki wata jijiya a tsakar kwanya sai jini ya fito ya malalo har zuwa qirji. Waxannan ayyuka, waxanda ba mai yin su sai bararo na daji wanda bai tava jin qanshin maraya ba, sai ko wanda guluwi ya raba shi da hankalinsa, ana yin su da sunan zaman makokin Hussaini da tunawa da shi kuma tuni har sun xauki sunan HUSSAINIYYAT.
Bukukuwan a da ana yin su ne a ranar goma ga watan Muharram kawai, amma daga baya sun zama ana shirya su a ko da yaushe, kuma an gina manyan ‘masallatai’ da qaburburan bogi inda ake zaman makoki tare da koke-koke, kuma mabiya suna kawo sadakoki.

Bukukuwan Ashura a Littattafan Shi’a na Farko:
Abin mamaki dangane da bukukuwan Ashura ba shi ne savawarsu ga Musulunci ba, ba shi ne ma savawarsu ga hankali da wayewa da ci gaban bil adama ba, babban abin mamaki shi ne savawarsu ga koyarwar malaman Rafilawa magabata da abin da yake rubuce a cikin littattafansu.
Manyan malaman Shi’a sun ruwaito haramcin irin waxannan bukukuwa da ayyukan jahilci daga Annabi (S.A.W) kamar yadda suka ruwaito shi daga imamansu, kuma wannan yana nan rubuce a cikin littattafansu waxanda ’yan Shi’a suka yarda da su kuma suke karanta su a kowane vangare na duniya. Ga misali; babban malaminsu mai suna Mirza Hussain Nuri Axxabarsi, ya fitar da hadisi cewa; Manzon Allah (S.A.W) ya ce: “Ba ya daga cikinmu wanda ya doki kumatu, ya keta wuyan riga.” Haka nan, babban malamin Hadisi a wurinsu, Muhammad bin Ya’aqub Alkulaini ya ruwaito daga imaminsu na shida, Ja’afar Sadiq, Allah ya rahamshe shi ya ce: “Wanda ya buga hannunsa a kan cinyarsa a yayin musiba, to aikinsa ya rushe.” To ina ga wanda ya mari kuncinsa ko ya daki qirjinsa ko ya fitar da jininsa, kamar yadda ’yan Shi’a suke yi. Har yau, Kulaini ya ruwaito daga imaminsu na biyar, Muhammad Baqir, Allah ya yi masa rahama ya ce: “Mafi tsananin rashin haquri shi ne kururuwa da kiran na-shiga-uku da marin fuska da qirji da cisgar gashi. Kuma wanda duk ya kafa makoki, to haqiqa ya bar haquri kuma ya yi nesa da tafarkinsa.”
Fatawar malaman Shi’a magabata ta zo da abin da ya dace da waxannan hadisai nasu. Malaminsu, Muhammad Hussaini Alshirazi, yana cewa: “Haramun ne dukan kumatu da cisgar gashi.” Kai malaman Shi’a ma sun ruwaito ijma’in magabatansu a kan haramcin irin waxannan abubuwa. Daga cikin waxanda suka naqalto ijma’in akwai Muhammad bin Makki Al’amili da Muhammad bin Hassan Annajafi.

Malaman Shi’a Sun Sava wa Imamansu:
Duk da waxannan ruwayoyi daga Annabi (S.A.W) da imamai da manyan shaihunan Rafilawa magabata da suke haramta bukukuwan Ashura da ayyukan jahilci da ke tattare da su, malaman Shi’a na zamani sun nace a kan gudanar da waxannan bukukuwa da fitar da fatawoyi da suke nuna halaccinsu.
Daga cikin irin waxannan fatawoyi akwai fatawar babban malaminsu wanda suke wa laqabi da Ayatullahil Uzma, Muhammad Hussain Anna’ini, inda yake cewa: “Babu shakka dangane da halaccin duka da hannaye a kan kumatu da qiraza har su yi ja ko su yi baqi (saboda duka). Kai yana ma halatta a yi duka da sarqoqi a kan kafaxu da baya har su yi ja ko su yi baqi. Kuma idan mari da duka ya kai ga fitar jini mara yawa, to duka babu laifi. Amma dangane da fitar da jini daga kai ta hanyar amfani da takobi da xan buda, to yana halatta idan ya zama ba a tsoron cutuwa, kuma zama babu karya qashi ko wata cuta da take biyo bayan fitar jini ga al’ada. Kuma wannan abu ne da mutanen da suka samu horo (na yadda ake fitar da jini daga kai xin) suka sani. Haka nan da mutum zai yi dukan ba ya cutarwa ga al’ada, amma sai aka yi rashin dace jinin da ya fita ya cutar, to wannan ma bai haramta shi. Sai ya zama kamar misalin wanda ya yi alwala ne, ko ya yi wanka, ko ya yi azumi ba tare da sa ran zai cutu ba, amma sai hakan ya cutar da shi”.
Sai mai hankali ya dubi wannan fatawa da abin da ta qunsa na abubuwan ta’ajibi.
1. Da farko dai malamin ya ce: “Babu shakka dangane da halaci.” Alhalin yana sane da hadisin Annabi (ruwayar Shi’a ba ruwayar Sunna ba), da maganar imamai biyu da fatawar magabatan Rafilawa da ijma’insu, duka a kan haramci. Idan malamin ya san waxannan abubuwa, to ni ban san abin da za mu kira shi ba. Sai mu qyale ’yan Shi’a su ba shi suna su da kansu. Idan kuma bai sani ba, to don me ake kira shi malami, har aka ba shi wannan qaton laqabi (Ayatullahil Uzma), irin na Khumaini, kuma aka xauki fatawarsa ake yaxa ta a cikin littattafai?
2. Na biyu, malamin ya ba da dama a yi duka da hannuwa da sarqoqi a kan kumatu da qiraza da kafaxu da baya har wajen ya yi ja, ko ya yi baqi, saboda duka. Shin a tsammaninka, mai karatu, wa malamin yake zato yana yi wa magana a lokacin da yake ba da wannan fatawa; mutane ko dabbobi?
3. Sannan malamin ba ya ganin laifi a fitar da jini daga kai ta hanyar amfani da takobi (ba wuqa ba, malam?) ko rodi, matuqar dai ba a fasa qashi ba. Kuma matuqar ba a ji tsoron wata cuta wacce take biyo bayan fitar da jini ba ga al’ada. Wataqila malamin yana nufin irin abin nan da likitoci suke cewa ‘infection’. Hoxi jam! Wani aiki sai guluwi. To ni ban san ta’aliqin da zan ti ba a nan; idan akwai xan Shi’a a kusa sai ya taimaka.
4. Sannan daga qarshe ga wani fiqihu mai zurfi. Da xan Shi’a zai fasa kansa da rodi jini ya zuba a ranar Ashura, saboda baqin cikin mutuwar Hussaini (R.A), kuma ya zama ba ya zaton zai cutu da hakan, amma sai aka yi rashin dace ya cutu xin, to da sai ya zama kamar wanda ya yi alwala da ruwan sanyi ba ya zaton zai yi mura, amma sai mura ta kama shi.
5. Malamin ya yi maganar waxansu da suka samu horo na yadda ake fitar da jini daga kai ba tare da hatsari ba. Na ga waxannan qwararru a talabijin da yadda suke tafiyar da aikinsu. Suna lalubar wata jijiya ne a tsakar kai, kamar yadda likita yake laluben jijiya idan zai xauki jini don gwaji, sannan sai su sa wan xan qaramin rodi mai kama da xan buda sai ka ji ‘qwas’. Sai kawai jini ya kwararo cikin sauqi. Wannan wani ci gaba ne da aka samu wanda ya kautar wa ’yan Shi’a haxarin amfani da takubba da wuqaqe.
Wani malamin Rafilawa da ya sava hadisin Annabi (S.A.W) ruwayar Shi’a ba ruwayar Sunna ba), ya sava umarnin imaman Shi’a, ya sava fatawar malaman Shi’a magabata, kuma ya keta ijma’insu don ya halasta bukukuwan Ashura shi ne shugaban Rafilawan duniya na wannan zamani kuma jagoran juyin juya hali na Iran, marigayi Ayatullah Ruhullah Khumaini.
Ga abin da yake faxa a cikin wasiyarsa ta qarshe ga ’yan Shi’a: “Lallai bukukuwan marin nan da kuke gani su ne suke nuna haqiqanin cin nasararmu. Saboda haka, a shirya bukukuwan makoki na tunawa da Hussaini a dukkan sassan qasa. Masu huxuba su aike da ta’aziyarsu kuma mutane su yi kuka. Ku yi ta yin bukukuwan mari da tarukan tunawa da Hussaini kamar yadda aka saba. Kuma ku sani rayuwar wannan al’umma ta ta’allaqa da waxannan bukukuwan da zaman makoki da taruka.”
Magajin Khumaini, mai jagorancin daular Iran na yanzu, Ali Khamna’i, ya qara tabbatar da wannan wasiya ya ce: “Akwai abubuwa da suke kusantar da mutane ga Allah kuma su qara qarfafa riqonsu da addini. Waxannan abubuwa sun haxa da bukukuwan ta’aziyya na al’ada. Kuma abin da Imam (yana nufin Khumaini) ya yi mana wasiya da shi na tsara bukukuwan ta’aziyya na al’ada shi ne shiga tarukan Hussainiyyat, da tuna Imam Hussaini da kukan rashinsa da dukan qirji a tarkuna ta’aziyya. Waxannan al’amura ne da suke qarfafa soyayya ga Ahalul Baiti. I, kuma lallai duka a kan kawuna da qiraza yana cikin wannan.”

Sanya Baqaqen Tufafi a Bikin Ashura:
Wani abu kuma da ’yan Shi’a suka sava wa imamansu da ijma’in malamansu shi ne sanya baqaqen tufafi, musamman a lokacin bukukuwan Ashura. Ingantattun ruwayoyi a cikin littattafan Rafilawa da suke izna da su sun taho da hanin sanya baqaqen tufafi, amma ’yan Shi’a suna sa irin waxannan tufafi a matsayin alamar baqin ciki da makokin Hussaini.
Ga misali, an ruwaito a littafin Man La Yahduruhul Faqih, xaya daga cikin littattafan Shi’a guda huxu mafiya inganci, daga Sarkin Musulmi Ali bin Abi Xalib (R.A) ya ce: “Kada ku sanya baqaqen tufafi domin su tufafin Fir’auna ne.” Babban malamin Rafilawa, Muhammad Rida Alhussaini Alha’iri ya ce: “Ya shahara a tsakanin ’yan’uwanmu mabiyan Imamiyya shahara mai girma, kai an ma yi ijma’i cewa makaruhi ne sanya baqaqen tufafi a cikin Salla da wajenta.” A cikin Salla da wajenta, yana nufin a kowane hali, a kowane yanayi.
Tare da wannan hani daga imamin Shi’a na farko, ma’asumi, wanda babu bambanci tsakanin maganarsa da ayar Alqur’ani a wajen Rafilawa, da kuma ijma’in malamansu, amma duk da haka ’yan Shi’a suna sanya baqaqen tufafi a lokacin bukukuwan Ashura wai don nuna baqin ciki da alhini da juyayin mutuwar Hussaini. Kai a yau ma baqaqen tufafi sun zama abin adon Rafilawa kamar yadda muke gani a wajen mazauna babbar qasar Shi’a a duniya, wato Iran.
Mun kawo wannan bayani domin mu nunawa masu yin Shi’a da gaske a nan qasar cewa, ’yan’uwansu na sauran vangarorin duniya su ba su xauki abin da gaske ba. Maimakon haka, son ransu suke bi, ba maganar Imami ko malamai ba.

Matan Shi’a da Bikin Ashura:
Mata ’yan Shi’a suna taka babbar rawa a wajen bukukuwan Ashura da zaman makokin shekara-shekara na Hussaini. Suna fita wajen jerin gwano na waxannan bukukuwa kuma su ne a kan gaba wajen kuka da marin kunci da cisgar gashi da sauransu. Hanin da aka ruwaito na wannan biki daga Annabi (S.A.W) da imamai da malaman Rafilawa ya game maza da mata, amma mun ware wannan sashe musamman don kawo ruwayoyin imaman Shi’a da suka gargaxi mata a kan irin ayyukan jahilci da suke faruwa a wajen waxannan bukukuwa saboda yadda matan Shi’a suke gaba-gaba a gudanar da bukukuwan. An ruwaito cewa, a lokacin da yaqi ya kaure a Karbala tsakanin mabiyan Hussaini (R.A) da abokan gabarsa, qanwarsa Zainab ’yar Ali, ta mari kuncinta, ta yaga tufafinta, kuma ta faxi sumammiya. Bayan da ta farfaxo, hankalinta ya komo jikinta, Hussaini (R.A) ya yi mata gargaxi. Ya ce: “Ya ke ’yar’uwata, ki ji tsoron Allah, ki nemi sayayayawa daga Allah. Ki sani cewa waxanda suke bayan qasa duka za su mutu, haka nan waxanda suke cikin sama ba za su wanzu ba. Kuma lallai komai halakakke ne sai zatin Allah Maxaukaki, wanda ya halicci halitta da qudurarsa… Ubana ya fi ni, uwta ta fi ni, kuma wana ya fi ni (amma duka sun mutu).” Ya ci gaba da yi mata wa’azi, yana tausar ta. Sannan ya ce mata: “Ya ke ’yar’uwata, idna aka kashe ni, kada ki yaga tufafi saboda ni, kada ki yakushi fuska saboda ni, kada ki ce kin shiga uku kin lalace.”
Haka nan, an ruwaito daga Abu Abdullahi Ja’afar Sadiq, imamin Shi’a na shida, yana fassara faxin Allah Maxaukaki, “Wala ya’asinaka fi ma’aruf.” Ya ce: “Ma’aruf shi ne kada su keta tufafi, kada su mari kunci, kuma kada su kira shiga uku”.

Azumi a Ranar Ashura:
Abu ne da aka sani cewa, Ahalus Sunna suna Azumi a ranar Ashura domin ya inganta a hadisi Annabi (S.A.W) ya azumce shi, kuma ya yi umarni da azumtarsa. Amma Rafilawa da suka mayar da ita ranar biki, sai suka qaryata wannan Azumi suka ce wai sarakan Banu Umayya ne suka yi umarni da shi don su hana mutane tunawa da Hussaini. Daga cikin masu faxin haka akwai malamin Shi’a na wannan zamani, wanda ya shahara da tsaurin kai ainun, wato Muhammad Tajjani Samawi.
Malaman Shi’a suna yin wannan magana tare da cewa suna sane da ruwayoyi daga imamansu da suke umarni da azumtar wannan rana. An ruwaito daga Ja’afar Sadiq wanda ya karvo daga mahaifinsa, Muhammad Baqir, ya ce: “Azumin ranar Ashura kaffarar shekara ne.” kafinsu, an ruwaito daga Ali bin Abi Xalib (R.A) ya ce: “Ku azumci ranar Ashura, tara da goma (ga wata), domin kiyayewa. Lallai shi (Azumin) kaffara ne ga shekarar da ta gabace shi. Idan xayanku bai san da azumin ba har ya ci abinci a ranar, to ya kame bakinsa.
Duba ka gani, mai karatu, yadda Sarkin Musulmi Ali, Allah ya qara masa yarda, ya qarfafa wannan Azumi da cewa ko mutum ya wayi gari bai san da shi ba, ya ci abinci, to ya kame bakinsa, ya cika azuminsa. Kuma wannan ruwaya malaman Rafilawa ne suka naqalto ta amma da yake ta sava son zukatansu, sai suka qeqashe qasa suka qaryata da ita, kuma suka lanqaya ma sarakan Banu Umayya don su fusata mabiyansu waxanda tuni sun sa musu qiyayyar sarakan Banu Umayya, kai har ma da qabilar Banu Umayya baki xayansu. Duba ka ga yadda ake yin addini; son zuciyar malamai da jahilcin mabiya.

Bikin Ashura a Nijeriya:
Rafilawan Nijeriya sun ara sun yafa, inda suke haxa gangami a ranar goma ga watan Muharram domin bikin tunawa da shahadar Hussaini a Karbala. Babu tabbas ko suna sane da waxancan ruwayoyi da muka kawo na hanin Annabi (S.A.W) da imamai ga irin wannan biki ko a’a. Dalili kuwa saboda yawancin ’yan Shi’ar qasar nan daga ’yan boko waxanda ba su iya sanin abu sai in ya biyo ta hanyar TRANSLATION ko TRANSLITERATION, sai jahilai tsantsa waxanda ba su iya rubutu da karatu ba. To ka ga irin waxannan zai yi wuya a yi musu shaidar cewa suna yin varna a bisa sani.
To sai dai abin da yake tabbas shi ne varna kam suna yin ta. Domin cikin abubuwan assha da bidi’o’i na bikin Ashura ba abin da ya rage musu sai TAXBIR kawai. Kuma kullum abin sai gaba yake yi. Allah ya sauqaqe.
Wani abin mamaki da takaici dangane da bikin Ashura a qarsar nan shi ne y adda wasu ’yan xariqa suke shiga ana yi da su. Ko da yake da ma wasu daga cikinsu suna da abin da ya yi kama da irin wannan biki, kamar ’yan xariqar Qadiriyya masu bikin waliyyai wanda suke yi a Kano a ranar 11 ga watan Rabi’us Sani na kowace shekara. Su kuwa ’yan Tijjaniyya waxanda ba su da irin wannan biki ga alama suna gab da mayar da bikin Maulidi ya zama irin sa. Tuni wannan ya fara a wasu biranen qasar nan.
Nasiharmu ga ’yan xariqa ita ce su sani cewa, ’yan Shi’a ba abokan tafiyarsu ba ne. Ko da yake tushensu na bidi’a xaya ne, to amma bidi’ar ’yan Shi’a ta fi tasu kaushi saboda miyagun aqidu da suke qudurewa waxanda cikin sauqi suna iya fitar da mutum daga Musulunci. Su kuwa ’yan xariqa Ahalus Sunna ne saboda sun yarda da Halifancin Khulafa’ur Rashiduna baki xayansu. Bugu da qari, babu mai zagin sahabin Annabi ko xaya a cikinsu (ko da yake sun fi damuwa in an zagi shainunnai), ba wanda ya y arda da ma’asumi bayan Annabi a cikinsu, ba wanda yake ganin Karbala ta fi Makka da Madina a cikinsu. Saboda haka kada su yarda da yaudarar ’yan Shi’a da taqiyyarsu. Su sani cewa wanda bai ga girman Abubakar da Umar ba, Allah ya qara musu yarda, to ba zai ga girman Shaihu Abdulqadir da Shaihu Tijjani ba. Daxa ballantana Inyas.
Don haka muke ganin ya zama wajibi ga ’yan xariqa su fito fili su barranta da ’yan Shi’a kuma kada su yarda wani abu ya haxa su. Muna roqon Allah Maxaukaki da ya shirye mu baki xaya. Ya raba mu da bin shaixan da son zuciya, amin.
Faxuwa da Riba a Mutuwar Hussaini
Mutuwar Hussaini a fagen fama da shahada da ya yi a hannun abokan gabarsa al’amari ne mai girma da ya faru a tarihin al’ummar nan wanda Allah ya xaukaki wasu mutane da shi ya qasqantar da wasu, wasu suka ci riba wasu kuma suka faxi warwas.
Mutum na farko da ya ci riba da wannan al’amari shi ne Hussaini shi da kansa saboda Allah ya ba shi shahada wacce zai xaukaki darajarsa da ita a lahira. Hussaini bai samu darajar rigaye zuwa Musulunci ba irin wadda Musulmin farko, kamar Abubakar da Umar da Usman da Ali da Xalha da Zubair suka samu. Bai gamu da cutatawar mushrikai ba irin wacce su Ammar bin Yasir da Suhaib Arrumi da Bilal da Sumayya suka gamu da ita. Bai xanxani xacin hijira ba irin wanda magabata suka xanxana kamar su Mus’ab bin Umair da Usman bin Maz’un da Abu Salma da Ruqayya xiyar Annabi da sauransu. Bai yi yaqi tare da Annabi ba saboda ko da Manzo ya koma ga Ubangijinsa duka shekarunsa ba su wuce shida ko bakwai ba. Bai yi jihadin ’yan ridda ba a zamanin Abubakar Siddiqu, tun da har aka gama waxannan yaqoqa shekarunsa ba su wuce tara ba. Haka nan, bai shiga jihadin buxe qasashe ba na zamanin Umar bin Khaxxab. Sabod ahaka darajoji masu yawa su kuvuce masa, amma sai Allah a cikin rahamarsa da hikimarsa ya musanya masa da shahda da ya karrama shi da ita. Don haka, Hussaini shi ne mutum na farko da ya ci riba da wannan al’amari.
Wasu kuma da suka ci riba da shahdar Hussaini a fagen fama su ne muminai na kowane zamani da suka xanxani baqin cikin mutuwarsa kuma suka tsaya a kan abin da Allah yake so, yake yarda da shi, ba su daxa ba, ba su raga ba. Suka ce: Innalillahi wa inna ilaihi raji’un. Waxannan su ma sun ci riba domin Allah ya jarrabe su da musifa kuma sun yi abin da Allah yake so bayinsa su yi a yayin da ya jarrabe su da musifa.
Amma waxanda suka yi asara da wannan al’amari suna da yawa. Na farko, kuma manyan masu asara, su ne waxanda suka kashe shi da hannayensu, wato kwamanda Umar bin Sa’ad da rundunarsa. Sai kuma gwamnan Kufa, Ubaidullahi bin Ziyad idan ta tabbata ya ba da umarni a kashe Hussaini ko ya yarda da kisansa. Sannan sai Yazidu xan Mu’awiyya shi ma idan ta tabbata cewa ya ba da umarni a aikata wannan ta’asa, ko ya yarda da ita, ko ya ji daxinta. Waxannan babu shakka sun yi asara, kuma hukuncinsu yana ga Allah.
1. Waxanda suka aike wa Hussaini da wasiqu suka gayyato shi zuwa Kufa amma suka basar da shi, suka gaza kare shi, suka bari abokan gabarsa suka kashe shi.
2. Waxanda suka ji ko suka karanta shahadar Hussaini sannan suka shiga raba laifi, a bisa rashin sani, ko kuma alal aqalli a bisa rashin tabbas, ga waxanda suke zato sun aikata ba daidai ba a cikin al’amarin, kuma suka xauki gaba da su, suna zagin su, suna la’antar su. Waxannan babu shakka sun yi ganganci kuma ba su kyautata aiki da faxin Allah ba: “Kuma kada ka bi abin da ba ka da ilimi game da shi. Lallai ne ji da gani da zuciya, duka waxancan (mutum) ya kasance daga gare shi wanda ake tambaya.” (Suratul Isra: 36).
3. Waxanda suka ji takaicin mutuwar Hussaini kuma suka wuce haddin Shari’a ta wajen aikata ayyukan jahilci da jahiliyya kamar bikin tunawa da kashe shi a duk shekara da kuka da kururuwa da kiran na-shiga-uku, ko suka sanya baqaqen tufafi, ko suka doki jikkunansu, ko suka mari kumatunsu, ko suka cizgi gashinsu, ko suka yaga rigunansu, ko suka fitar da jini daga jikkunansu, don baqin ciki. Haka nan da masu ziyarar shirka zuwa kabarin Hussaini da masu zaman makoki ba qarewa, da sauran nau’o’in jahilci masu vatan vakatantan, “waxanda aikinsu ya vace a rayuwar duniya, alhali kuma suna zaton lallai ne su, suna kyautata (abin da suke gani) aikin qwarai ne.” (Suratul Kahf: 104).
Muna roqon Allah ya tsare mu tavewa. “Ka ce Ya Allah, Mai qaga halittar sammai da qassai, Masanin gaibi da bayyane. Kai ne ke yin hukunci a tsakanin bayinka a cikin abin da suka kaasnce suna sava wa juna a cikinsa.” (Suratuz Zumar: 46). Tsarki ya tabbatar maka, ya Ubangiji tare da godiya a gare ka. Ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai kai. Ina neman gafararka, ina tuba zuwa gare ka.

MANAZARTA
A. LITTATTAFAN AHALUS SUNNA:
Abdurrahman bin Jauzi, Alraddu Alal Muta’assibil Anid Almani’i min Zammi Yazid, Darul Kutubil Ilmiyya, Beirut, 1426/2005.

Abubakar bin Arabi, Al’awasim Minal Qawasim, Alqahira, 1375.

Ahmad bin Taimiyya, Majmu’ul Fatawa, Riyad, 1381.

Ahmad bin Taimiyya, Minhajus Sunnatin Nabawiyya, Riyad, 1406/1986.

Ibnul Athir, Alkamil Fit Tarikh, Beirut, 1385/1965.

Ibn Hajar Alhaitumi, Assawa’iqul Muhriqa Fir Raddi ala Ahlil Bida’i wal Zandaqa, Alqahira, 1385/1965.

Ibn Kathir, Albidaya wal Nihaya, Beirut, 1974.

Kamal bin Humam, Almusamara fi Sharhil Musayara, Alqahira, 1347.

Mahmud Aalusi, Ruhul Ma’ani fi Tafsiril Qur’anil Azim was Sab’il Mathani, Dimashqa.

Muhammad bin Isma’il Albukhari, Sahihul Bukhari, Darul Jil, Beirut.

Muhammad bin Jarir Axxabari, Tarikhul Umami wal Muluk, Darul Ma’arif, Misra, 1962.

Muhammad bin Muhammad Algazali, Ihya’u Ulumiddin, Darul Fikr, 1400/1980.

Muhammad Rashid Rida, Tafsirul Manar, Misra, 1375.

Muhammad bin Usman Azzahabi, Siyaru A’alamil Nubala, Mu’assasatul Risala, 1401/1981.

Muhammad bin Usman Azzahabi, Mizanul I’itidal fi Naqdir Rijal, Misra, 1383/1963.

Sa’aduddin Attaftazani, Sharhul Aqidatin Nasfiyya, Astana, 1277.

Yusuf bin Fargali, Tazkiratu Khawasil Umma fi Khasa’isil A’imma, Maxba’atun Najaf, 1383/1964.

B. LITTATTAFAN RAFILAWA:
Abbas

Alqummi, Muntahal Aamal fi Tarikhin Nabiyyi wal Aal, Addarul Islamiyya, Beirut, 1414.




Kuna iya tuntu6ar mu ta wadannan hanyoyin
Abdul-majid Ibn Nuh ta face book

KO TA SHAFIN MU NA FALALAR SAHABBAI DAGA BAKIN IMAMAI TA FACE BOOK.

Ko ta watsAp A 07063276717
Bugo mana waya ta nan
Bugo mana waya ta nan
Bugo mana waya ta nan
Ko ta Email A

Home


Copyright © 2014 - 2015By:- Abul-majid Ibn Nuoh Powered by- Basheer journalist sharfadi


Pair of Vintage Old School Fru